Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Corona: Amurka ta buɗe iyakokin ta ga bakin haure bayan shafe watanni 20 a rufe

Published

on

Ƙasar Amurka ta bude iyakokin ta na sama da kasa ga baki ‘yan kasashen waje wadanda suka karbi allurar rigakafi, bayan rufe iyakokin da tayi na tsawon watanni 20 domin yaki da annobar Korona.

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ne ya kafa dokar hana baki shiga kasar a farkon shekarar 2020, wadda ta samu goyan bayan shugaba Joe Biden da ya gaje shi domin dakile yaduwar cutar.

A watan Maris na shekarar 2020 shugaba Trump ya sanar da rufe iyakokin kasar ga baki daga kasashe da dama cikin su harda masu zuwa daga Turai da Birtaniya da China da India da kuma Brazil.

Wannan haramci na Amurka ya gamu da suka musamman daga kasashen Turai da kuma makociyar ta dake Canada da Mexico.

Sanarwar gwamnatin Amurka ta ce janye haramci zai shafi baki daga kasashe sama da 30, amma kuma hukumomi za su ci gaba da sanya ido domin tabbatar da cewar masu shiga kasar sun karbi allurar rigakafi sau biyu da kuma shaidar cewar basa dauke da cutar Korona.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!