Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Al’umma su dinga zaban shugabanni na gari – Sarkin Kano mai murabus

Published

on

Sarkin Kano murabus Malam Muhammadu Sanusi na biyu ya bukaci al’ummar kasar nan da su rika zaban shugabanni na gari ba tare da la’akari da jam’iyya ba.

Malam Muhammadu Sanusi na biyu ya ce zaben nagari shi ya fi dacewa maimakon rika zabin duk wanda jam’iyya ta tsayar a zabe.

Sarkin na Kano ya bayyana hakan ne a garin Kaduna lokacin da wata kungiya me rajin tallata hajarsa mai suna ‘’Sanusi Lamido Sanusi for President 2023 support Group’’ suka kai masa ziyara.

Sarkin Kano na goma sha hudun dai ya kai ziyara mako guda ne jihar Kaduna wanda shine ziyararsa ta farko zuwa arewacin kasar nan tun bayan saukeshi daga mulki a watan Maris.

Tun farko da yak e bayyana makasudin ziyarar tasu jagoran kungiyar yada manufa ta Sanusi Lamido Sanusi 2023 dr. Suleiman Shuaibu, ya bayyana irin nasarori da sarkin na Kano murabus ya samu lokacin da yak e aiki a matsayin dalilan da suka dacewar ya cancanci jagorantar kasar nan.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!