Labarai
Al’umma su guji zuba shara a magudanan ruwa – REMASAB
Hukumar kwashe tsara ta jihar Kano,ta bukaci al’umma su dinga zuba shara a inda aka tanada tare da kaucewa zubawa a magudanan ruwa musamma ma a wannan lokacin na damuna
Darakatan ayyukan yau da kullum na hukumar, Alhaji Shu’aya’u Abdulkadir Jibrin ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala shirin ‘Barka Da Hantsi’ na nan freedom radio wanda aka tattauna akan matsalar muhali da ake fuskanta.
Ya kuma kara da cewar babban abinda yake haifar da guebacewar muhali a jihar nan baya rasa nasaba da yadda mutane ke tara shara ko tare kasa a hanyoyi wanda hakan ke janyo toshewar magudanan ruwa kuma hakan kan haifar da ambaliyar ruwa.
Daraktan ta kuma bayyana cewar dukkan wanda hukumar da kama da wannan dabi’a ta zuba shara ko tare kasa a wuraran daba su dace ba zata hukuntashi dai-dai da laifin da ya aikata.
Shu’aya’u Abdulkadir Jibrin ya kuma shawarci al’umma dasu rinka sanar musu,inda zasu yi aikin gayya a unguwanin su, domin basu gudunmawar kayan aiki.
You must be logged in to post a comment Login