Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Nigeria: Karin mutum 354 sun kamu da cutar Corona jiya Alhamis

Published

on

Cibiyar dakile cutuka masu yaduwa ta kasa NCDC ta ce, an samu karin mutane 354 da suka kamu da cutar Corona jiya Alhamis a jihohi 16 na kasarnan da birnin tarayya Abuja.

NCDC ta sanar a daren Alhamis ta shafinta na Twitter cewar karin da aka samu na nufin adadin wadanda suka kamu da Corona ya kai 45,244, daga ciki kuma an sallami mutane 32,430 da suka warke daga cutar a fadin kasarnan.

Haka kuma cutar tayi sanadiyyar ajalin mutum 930.

NCDC ta kuma sanar a babban shafinta na Internet cewa, zuwa yau Jumu’a masu Corona 11,884 ne suka rage wadanda ke jinyar cutar a sassan kasarnan.

A nan Kano ma, gwamnatin Kano ta ce, an samu karin mutum 9 dauke da cutar cikin mutane 270 da aka yiwa gwajinta a jiya Alhamis.

Sannan kuma an sallami wasu mutane 16 da suka warke daga cutar ta Corona.

Ma’aikatar lafiya ta Kano ta ce, mutane 1,608 ne aka tabbatar sun kamu da Corona a fadin jihar, kuma daga ciki 1,291 sun warke sarai, sai mutum 53 da cutar ta hallaka.

Gwammatin jihar Kaduna kuwa ta sanar da samun karin mutane 23 da suka kamu da cutar, cikin mutane 102 da aka yiwa gwaji jiya Alhamis.

Gwammatin jihar ta sanar a shafinta na Twitter cewar, karin mutane 23 sun warke daga cutar a jihar.

Zuwa yanzu dai mutum 1,530 ne aka tabbatar sun kamu da cutar a jihar, yayin da aka sallami 1,335 daga ciki bayan da suka warke.

Haka kuma mutane 12 ne suka rasa ransu sanadiyyar cutar a jihar ta Kaduna.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!