Labarai
Al’umma su kwantar da hankulan su-IPMAN
Kungiyar dillalan man fetur ta kasa IPMAN ta ce ta dauki matakai da dama wajen dakile matsalar karancin man fetur da aka saba fuskanta a duk karshen shekara a kasar nan, a don haka ma al’umma su kwantar da hankalinsu.
Shugaban kungiyar dillalan man fetur din reshen Jihar Kano Bashir Ahmad Dan-Malam ne ya bayyana hakan yau jim kadan bayan kammala shirin Barka da Hantsi na nan Freedom Radio, da ya mayar da hankali kan karancin man fetur din ake fuskanta duk karshen shekara.
Ya kuma kara da cewa akwai matakai da gwamnati ta dauka da suka nuna cewar ba za a samu wannan matsala ba a wannan lokaci, sakamakon zaman da kungiyar keyi dasu domin tattauna al’amarin.
Bashir Dan-Malam ya kuma kara da cewa suna goyon bayan batun matakin gwamnatin tarayya na hana gidajen man fetur dake kusa da iyakokin kasar nan daukar mai, sai dai akwai bukatar gwamnatin ta yi abinda ya kamata domin akwai al’umma da dama da suka sanya kudadensu a ciki.
Kungiyar manyan dillalan man fetur DAPPMA ta janye yajin aikin da zata fara a yau
Fadar shugaban kasa ta musanta zargin cire naira biliya daya na rarar man fetur
Kamfanin NNPC sun fara safarar man fetur kasashen Burkina Faso da Mali da Cote d’Ivore
Ya kuma yi kira da mutane da a ko yaushe su kasance masu yin biyayaya ga dokokin da kasa ta gindaya musu.