Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Al’ummar Bachirawa sun shiga tasku sanadiyyar yajin aikin da ƴan garuwa suka tsunduma

Published

on

Al’ummar yankin Bachirawa da ke nan Kano sun shiga hali ni ƴa su, sanadiyyar rashin samun ruwa a unguwar.

Ƙarancin ruwan da aka wayi gari da shi a ranar Lahadi ya biyo bayan yajin aikin sai baba ta gani da masu sayar da ruwa a unguwar suka tsunduma.

Wasu mazauna unguwar sun shaida wa Freedom Radio cewa, har kusan ƙarfe 11 na safe, ba su samun ruwan yin girki ba, ballantana na yin wanka da wanke-wanke.

Wata mata mai suna Hajiya Nafi ta ce, “Tun safe babu ruwa, ga yara duk ban yi musu wanka ba, ga zafi ana ciki”.

Ita kuwa Inna Iliyasu cewa ta yi, “Tun safe har yanzu ina son dafa shayi amma babu ruwa, yanzu haka ina fama da matsalar banɗaki amma bani da ruwa”.

Ƴan mata ma sun shiga tasku sanadiyyar wannan yajin aiki kamar yadda wata Aisha Tasi’u ta bayyana.

A cewar ta, da alama yau babu kwalliya matuƙar ba a samu daidaito da masu garuwan ba.

Karin labarai:

Ganduje ya taimaka mana da ruwan sha a yankin mu – Mai garin Gama

Ganduje zai yi wa matsalar ruwan sha a Kano diban karen mahaukaciya

Me ya haifar da shiga yajin aikin?

Wasu masu sana’ar sayar da ruwa a unguwar sun shaida wa Freedom Radio cewa, masu tankin ruwa sun yi musu ƙarin farashi.

A baya ana sayar musu da jarka 11 a kan Naira 60, jarka 14 kuma a kan Naira 70.

Amma a yanzu an koma sayar da Jarka 11 Naira 80, yayin da Jarka 14 kuma ake sayar wa a kan Naira 100.

Hakan ne, ya sanya suka ƙara kuɗin jarkar ruwa daga Naira 20 zuwa 30, wanda kuma basu samu karɓuwa daga jama’a ba.

Ko da muka tuntuɓi wani cikin masu tankin ruwa a unguwar da ya nemi a sakaya sunan sa, ya ce su ma ai sun samu ƙarin farashin kuɗin man Diesel zuwa Naira 265.

A ƙalla unguwanni 9 ne wannan yajin aikin ya shafa waɗanda suka haɗar da layin mai gari, da Bachirawa Kwata, da Asibitin Tafasa.

Sai kuma Gadar Madugu da layin Yarbawa sai unguwar Gidan Ɗan Gaske da Titin Ƙasa da kuma Titin Zango, sai layin sararriyar Kuka.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!