Labaran Kano
Al’ummar garin Kiru sun koka kan matsalar rashin asibitoci da makarantu
Wata kungiya mai rajin cigaban garin Kiru wato Kiru Development Community Forum ta ce suna fuskantar matsaloli da dama da ke addabar cigaban gari da suka hadar da harkar lafiya, ilimi da kuma wutar lantarki.
Shugaban kungiyar Malam Aliyu Isyaku ne ya bayyan hakan yayin wata ziyara da suka kaiwa kwamishina ilimi ta jihar kano a jiya Talata.
Malam Aliyu Isyaku ya bukaci kwamishian da ya sanya hannu wajen magance musu matsalolin da suke fuskanta ta hanyar kai musu kwararrun malamai a makarantun su da likitoci a asibitocin su.
Ya kuma kara da cewa suna bukatar likitoci da kuma gyara musu makarantu domin cin ribar demokradiya.
A nasa bangaren kwamishinan ilimi na jihar Kano ya ce ya karbi dukkanin kokensu tare da shan alwashin mika bayanan nasu zuwa inda ya kamata domin a magance musu matsalolin.
Ya ce za su zauna da takwaransa na ma’aikatar lafiya domin duba batun da suka zo dashi a bangaren lafiya da na ilimi domin a kawo musu daukin da suke bukata na gyara makarantu da asibitocin a garin na Kiru
Wakiliyar mu Hafsat Abdullahi Danladi ta ruwaito cewa taron ya samu halatar Dagacin garin na kiru da sauran manya mutane.