Connect with us

Labarai

Za a bude makarantu domin jarrabawar NABTEB a Kano

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da umarnin hanzarta bude makarantun kwalejojin fasaha guda shida a jihar domin bai wa daliban ajin karshe na sakandire damar rubuta jarrabawar kammalawa ta NABTEB.
Kwamishinan ilimi na Jihar Kano Malam Muhammad Sanusi Kiru ne ya bayar da umarnin hakan bayan samun amincewar gwamna Abdullahi Umar Ganduje, biyo bayan bukatar hakan da kwamishinan ya nema daga wurin gwamnan.
Muhammad Sanusi Kiru ya kara da cewa gwamnatin Jihar Kano ta amince da a gaggauta biyan kudin jarrabawar daliban ‘yan ajin karshe wato SSS3 domin ba su damar rubuta jarrabawar.
Wata sanarwa da jami’in yada labarai na ma’aikatar ilimi ta Jihar Kano Aliyu Yusuf ya fitar da yammacin yau, ta ce gwamnatin ta ware kudi sama da naira miliyan 16 domin ciyar da daliban da ma sauran bukatu wajen ganin an samu nasarar rubuta jarrabawar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!