Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Al’ummar garin Kiru sun koka kan matsalar rashin asibitoci da makarantu

Published

on

Wata kungiya mai rajin cigaban garin Kiru wato Kiru Development Community Forum ta ce suna fuskantar matsaloli da dama da ke addabar cigaban gari da suka hadar da harkar lafiya, ilimi da kuma wutar lantarki.

Shugaban kungiyar  Malam Aliyu Isyaku ne ya bayyan hakan yayin wata ziyara da suka kaiwa kwamishina ilimi ta jihar kano a jiya Talata.

Malam Aliyu Isyaku ya bukaci kwamishian da ya sanya hannu wajen magance musu matsalolin da suke fuskanta ta hanyar kai musu kwararrun malamai a makarantun su da likitoci a asibitocin su.

Ya kuma kara da cewa suna bukatar likitoci da kuma gyara musu makarantu  domin cin ribar demokradiya.

A nasa bangaren kwamishinan ilimi na jihar Kano ya ce ya karbi dukkanin kokensu tare da shan alwashin mika  bayanan nasu zuwa inda ya kamata domin a magance musu matsalolin.

Ya ce za su zauna da takwaransa na ma’aikatar lafiya domin duba batun da suka zo dashi a bangaren lafiya da na ilimi domin a kawo musu daukin da suke bukata na gyara makarantu da asibitocin a garin na Kiru

Wakiliyar mu Hafsat Abdullahi Danladi ta ruwaito cewa taron ya samu halatar Dagacin garin na kiru da sauran manya mutane.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!