Ƙetare
Ambaliyar ruwa ta hallaka mutane 47 tare da lalata fiye da gidaje 56,000 a Nijar

Hukumomi a kasar Nijar sun ce ambaliyar Ruwa ta hallaka mutame 47 tare da raba fiye da mutum 56,000 da gidajensu a Jamhuriyar Nijar.
Ambaliyar ta shafi gidaje 7,754 a cikin unguwanni da ƙauyuka 339, in ji hukumar tsaron fararen hula ta ƙasar.
Wasu mutane 30 sun mutu bayan gidajensu sun rushe yayin da mutne 17 suka nutse a ruwa.
Haka kuma, a cewar hukumar, ambaliyar ta raunata mutum 70 ta kuma haddasa mutuwar dabbobi 257.
Sai dai, Kwamiti na ƙasa da aka ɗora wa alhakin hana ambliya ya ce ya fara raba tallafin abinci ga iyalai 3,776.
You must be logged in to post a comment Login