Labaran Kano
Ambaliyar ruwa ya shafi wasu sassan jihar Kano
Mutane unguwar Kurna Asabe a yankin karamar hukumar Ungogo a cikin birnin Kano, na cigaba da kokawa kan yadda rashin magudanar ruwan ke yi musu barazanar ambaliyar ruwa.
A cewar Mazauna yankin da zarar sun ga hadari ba su da kwanciya hankali sakamakon fargaba ambaliya ruwa da suke tsunta Kansu a ciki.
Sun kuma ce, a duk lokacin da aka yi mamakon ruwan sama layukan unguwar na cika da ruwa, wanda ke tilastawa ruwan shiga gidajen su har ya haddasa rushe gidaje, ya yin da wasu kuma ke tafka asara dukiya.
Wasu mazauna yankin sun Freedom rediyo cewa, “Magudanan ruwan mahada ce da unguwanni kusan guda hudu kasancewar hakan ya haifar da karancin su.
Munyi kokarin ji ta bakin hukumar tsara birane ta jihar Kano KNUPDA amma hakar mu bata cim ruwa ba, inda jami’i hulda da jama’a na maikata ya bayyana mana cewa, Shugaban hukumar ya yi tafiya akan haka ne mu tutube shi ta wayar tarho amma wayar sa bata shiga ba.
Wakiliyar Hafsat Danladi ta rawaito cewar mazauna unguwar Kurna Asabe Layin masallacin na fatan cewa, mahukunta za su kai musu dauki.
You must be logged in to post a comment Login