Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ambaliyar ruwa ta tilasta wa mazauna wasu unguwanni yin hijira a Kano

Published

on

Wasu mazauna unguwannin Medile, Ɗanmaliki da Bechi a ƙaramar hukumar Kumbotso sun yi ƙaura daga gidajensu sakamakon ambaliyar ruwa.

Mamakon ruwan sama da aka tafka a ranar Asabar, ya cinye gidaje da dama a yankunan unguwannin.

Wasu mazauna unguwannin da lamarin ya rutsa da su sun shaida wa Freedom Radio cewa, ruwan ya musu mamaya ta yadda har saida aka riƙa tsamo wasu daga cikin ƴaƴansu daga ciki.

Alhaji Shu’aibu Bechi shi ne Mai Unguwar Bechi ya ce, dama a kan fuskanci wannan matsala a duk lokacin damuna, kasancewar ruwa yana kwaranyowa daga maƙotan yankuna zuwa unuwar.

Tun a baya dai, hukumar lura da yanayi ta ƙasa ta yi hasashen yiwuwar samun ambaliyar cikin wannan mako a wasu jihohi, ciki har da Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!