Labarai
Amfani da fasahar zamani zai taimaka wajen magance matsalar tsaro -Dakta Sani Lawan Malumfashi
An bayyana rashin amfani da fasahar zamani yadda ya kamata a matsayin dalilan da suke habaka rashin tsaro a fadin Nijeriya.
Wani masanin halayyar dan adam Dakta Sani Lawan Malumfashi wanda kuma malami ne a sashen nazarin halayyar dan adam da ke Jami’ar Bayero dake Kano ne ya bayyana hakan ta cikin shirin Barka da Hantsi na tashar Freedom Radio.
Ya ce matukar aka yi amfani da sababbin dabarun fasahar zamani, to za a samu sauki wajen yaki da manyan matsalolin tsaro da kasar nan ke fuskanta musamman fashi da makami da satar mutane.
Shi kuwa Kyaftin Abdullah Bakoji mai ritaya ya alakanta matsalar garkuwa da mutane da rashin tsari mai kyau wajen mallakar makamai.
Dakta Sani Lawan Malumfashi da Kyaftin Abdullah Bakoji sun yi kira ga hukumomin tsaron kasar nan da sauran masu ruwa da tsaki da su hada hannu wuri guda don kawo karshen matsalolin da suka addabi al’ummar kasar nan.