Connect with us

Labarai

Amnesty ta bukaci gwamnatin tarayya ta girmama ƴancin tsoffin ƴan sanda na yin zanga-zanga

Published

on

Ƙungiyar kare hakkin Dan-adam ta Amnesty International, ta ce, girmamawa da mutuntawa tsofaffin ƴan sandan Najeriya suka cancanta da su ba wulaƙanci ba.

 

Amnesty ta bayyana haka ne a shafinta na Facebook da yammacin ranar Lahadi, inda ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta girmama ƴancin da tsofaffin jami’an tsaron ke da shi na gudanar da zanga-zangar lumana saboda matsalar da suke fuskanta game da fansho.

 

“Matsalar da tsofaffin ƴansandan suke fuskanta a bayyane yake, kuma an daɗe ana watsi da ita.

Wannan ya sa yin ritaya ya zama abin tsoro ga ƴansanda. Bayan ɗaukar lokaci suna aiki, tsofaffin ƴansandan da iyalansu na fama da abin da suka kira “biyan fansho na ganin-dama.”

 

“A watan Janairun shekarar 2025 ne aka biya wasu haƙƙoƙin tsofaffin ƴansandan baya sun yi zanga-zanga.

Lallai ba ƙaramin abin kunya ba ne a ce sai sun yi zanga-zanga za a biya su haƙƙoƙinsu yadda ya dace.

Dole gwamnatin Najeriya ta yi abin da ya dace wajen magance cin hanci da ya jefa tsofaffin ƴansandan nan cikin damuwa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!