Ƙetare
Amurka ta bukaci ‘yan kasar ta da su yi gaggawar ficewa daga Venezueala

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta yi kira ga ‘yan kasar da ke Venezueala su gaggauta ficewa daga kasar.
Matakin na zuwa ne bayan da ma’aikatar ta ce ta samu rahotonnin yunkurin wasu kungiyoyin masu dauke da makamai na tare wasu hanyoyi a kasar tare da duba motocin Amurkawa da na mutanen kasashen da ke goyon bayanta.
Sanarwar na zuwa ne mako guda bayan sojojin Amurka sun kai hari kasar tare da da kama shugaban kasar, Nicolas Maduro da matarsa, inda suka tafi da su Amurka, don gurfanar da su a gaban kotu.
Shugaba Trump ya ce a yanzu kasarsa ce ke juya akalar kasar Venezueala tare da hadin gwiwar gwamnatin rikon kwarya.
To sai dai har yanzu makusantan Nicolas Maduro ne ke iko da jami’an tsaron kasar.
You must be logged in to post a comment Login