Labarai
Amurka ta ja kunnan gwamnatin rikon kwarya ta kasar Mali
Amurka ta shawarci gwamnatin rikon kwarya ta kasar Mali da ta mutunta yarjejeniyar da suka cimma da kungiyar raya tattalin arzikin yammacin kasashen Afrika ta ECOWAS.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Misis Morgan Ortagus ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta fitar.
Ortagus ta ce gwamnatin Amurka na bukatar ganin kasar Mali ta koma kan tsarin mulkin dimokradiyya, wanda hakan ba zai yi wu ba sai gwamnatin da aka kafa ta girmama yarjejeniyar da aka yi da ita.
Ta cikin sanarwar, gwamnatin Amurka ta kuma bukaci kasar ta Mali da ta guji keta hakkokin fararen hula ko duk wani nau’in cin zarafin bil’adama a wannan dan tsakani.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Amurka ta kara da cewa muhimmin abinda jami’an tsaron kasar ta Mali za su mayar da hankali a kai bai wuce kawo karshen matsalolin tsaron kasar ba.
You must be logged in to post a comment Login