Labarai
An ƙaddamar da sabon masauki da wuraren zuba jari ga Musulmin Najeriya a Makkah

An ƙaddamar da sabon ginin masauki da wuraren zuba jari da aka tsara musamman domin al’ummar Musulmai ‘yan Najeriya a birnin Makkah, kusa da Masallacin Harami.
Wannan muhimmin shiri mai suna King Salman Gate Project, wanda Yarima mai jiran gado kuma Firayim Ministan Saudiyya, Mohammed bin Salman, ya sanar da shi kwanan nan, na daga cikin manyan matakai wajen bunƙasa yankin tsakiyar Makkah da ke jawo hankalin mahajjata daga sassa daban-daban na duniya.
Yariman, wanda kuma shi ne Shugaban Hukumar RUA AlHaram AlMakki, ya bayyana cewa, aikin zai ƙunshi wuraren ibada sama da dubu dari tara 900,000, tare da ingantattun hanyoyin sufuri na jama’a domin sauƙaƙa zirga-zirgar masu zuwa yin ibada.
Manufar aikin ita ce ta inganta hidimar mahajjata, da sauƙaƙa musu damar isa Masallacin Harami, tare da samar da ayyukan yi sama da dubu dari uku 300,000 daga nan zuwa shekara ta 2036.
You must be logged in to post a comment Login