Labarai
An aike da Mu’azu Magaji zuwa asibiti kafin fara shari’a
Kotu ta bada umarnin mayar da tsohon kwamishinan Ayyuka na Jihar Kano Injiniya Mu’azu Magaji Ɗan Saruniya zuwa Asibitin ƴan sanda domin kula da lafiyar sa.
Alkalin kotun majistare mai lamba 58 ƙarƙashin mai shari’a Aminu Gabari ce ta bada umarnin bayan gurfanar da shi a gabanta.
Lauyan Gwamnati kuma mai gabatar da ƙara Barista Wada A. Wada shi ne ya nemi a karanto masa tuhumar nan take Lauyansa Barista Gazzali Datti Ahmad ya roki kotu da ta Dakata da batun karanta tuhumar.
Har ma yace wanda yake karewar yana cikin mawuyacin halin na yadda kunnuwansa suka sami matsala sakamakon raunin daya samu dai dai lokacin da Jami’an tsaro suka kamashi a Abuja.
Nan dai a kai musayar yawu tsakanin lauyoyin daga ƙarshe Kotu ta mayar da shi Asibiti.
Bayan fitowa daga kotun Wakilin Freedom Radio Aminu Abdu Baka Noma ya zanta da Lauyan Mu’az Magaji wato Barista Gazzali Datti Ahmad inda ya ce “ƴan sanda sun kama Mu’azu da motar gida bata aiki ba, kuma suna ƙoƙarin kama shi yayi tunanin masu garkuwa da mutane ne don haka yaji ciwo a kunne da hannu”.
“Wannan ne muka nemi a ɗage karanto masa laifin sa har sai ya samu lafiya, kuma ba wani ne ya shigar da ƙara ba illa gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje kan zargin da yayi na cewa Mu’azu ya wallafa wani hoto da ya shafi martabarsa a shafinsa na Facebook”.
Lauyan ya ce, za su yi duk mai yiwuwa na ganin sun samu nasara duk da cewa laifin da ya aikata ya ci karo da doka.
You must be logged in to post a comment Login