Kiwon Lafiya
An bude sabon ginin da Isah Inuwa ya gina a Asibitin Danbatta
Shugaban majalisar Malamai na jihar Kano, Malam Ibrahim Khalil, ya ce babban abinda Allah subhanawu-wata’alakeso shine taimakon al’ummar da basu dashi.
Malam Ibrahim Khalil ya bayyana hakan ne yayin bude sashin kula da lafiyar kana nan Yara da na mata masu Juna biyu a babban Asibitin garin Danbatta da Alhaji Isah Inuwa Muhammad ya gina, a matsayin sadakatul Jariya ga mahaifiyar sa Marigayiya Hajiya Asma’u Usman Danbatta.
Malam Ibrahim Khalin ya ce da mawadata na yin ayyukan taimakon al’umma yadda ya kamata baza’a tsinci Kai a halin da ake ciki ba a yanzu.
An ƙaddamar da makarantar da iyalan marigayi Magaji Ɗanbatta suka buɗe
A jawabin sa Alhaji Isah Inuwa Muhammad, lokacin da mahaifina sa Inuwa Muhammad ke bude sashin a yau Asabar 11 ga watan Satumbar shekarar 2021, ya ce duba da yadda al’umma ke bukatar taimako a bangaren kula da lafiya yasa ya gina gurin kuma ya badashi ga gwamnati domin Allah ya Kai ladan ga mahaifiyar sa Marigayiya Hajiya Asma’u Usman Danbatta.
Ya ce ” an zuba kayan zamani a sashin na kula da lafiya da suka hadar da abin da ke taimakawa mara lafiya shakar iska a kowanne Gado”.
Ya kuma ce an zuba gadaje na zamani da kujerun zamani a ofisoshi da kayan aiki a ko Ina.
A jawabin shi gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da kwamishinan lafiya ya wakilta Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa godiya ya yi ga Isah Inuwa Yahaya bisa kokarin da ya yi tare da tabbatar da cewa gwamnati za ta kula da gurin yadda ya kamata.
You must be logged in to post a comment Login