Labarai
An cafke Budurwa mai garkuwa da mutane a Kano
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta yi ƙarin haske kan masu garkuwa da mutane da ta cafke a nan Kano.
Lamarin ya faru ne a ranar Jumu’ar da ta gabata, inda ƴan sanda suka bankaɗo maɓoyar masu garkuwar a Unguwar Jaba ta ƙaramar hukumar Ungogo.
Jami’in hulɗa da jama’a na ƴan sandan Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatarwa da Freedom Radio faruwar lamarin.
Ya ce, an yi bata-kashi tsakanin ƴan bindigar da masu garkuwar kafin daga bisani suka yi nasarar cafke su ba tare da samun ko ƙwarzane ba.
Karin labarai:
An bankaɗo maɓoyar masu garkuwa da mutane a Kano
Garkuwa da mutane: Ƴan Kasuwar Kwari na tattara kuɗin fansa
Kiyawa ya ce, an kama maza uku da mace ɗaya mai suna Maryam wadda ta ƙware wajen garkuwa da mutane.
An kuma same su da bindiga AK47 da alburusai.
Binciken ƴan sanda ya gano cewa, Maryam ta karɓi hayar gidan a kan Naira dubu ɗari shida, a cewar Kiyawa.
Sannan ta jima tana yin garkuwa da mutane, tun bayan da jami’an tsaro suka kashe mijinta wanda ta ce, ɓarawon shanu ne a jihar Zamfara.
Maryam ta kuma ce, a baya-bayan nan ma ta yi garkuwa da wani saurayinta a nan Kano.
Kiyawa ya kuma ce, sauran waɗanda aka kama biyu daga ciki ba ƴan jihar Zamfara.
You must be logged in to post a comment Login