Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

KannyWood

Kun san dalilan da suka sanya aka garkame Sadiya Haruna a gidan yari?

Published

on

Kun san dalilan da suka sanya aka garkame Sadiya Haruna a gidan yari?

Biyo bayan da Rundunar ‘yansanda ta jihar Kano ta tabbatar da kame Sadiya Haruna shahararriyar jarumar nan ta soshiyal midiya, a kwanakin baya.

Har ma Kakakin rundunar ‘yansanda jihar Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatarwa da Freedom Radio cewa ‘yansanda na tsare da Sadiyan sakamakon korafin da jarumin fina-finan Hausa Isa I. Isa yayi kan na zargin taci zarafinsa da kuma bata masa suna, a kafafan sada zumunta da ma duniyar baki daya.

Sai dai kuma a kwanakin baya ne Fitacciyar ‘yar soshiyal midiyan a kafar sadarwa ta Instagram Sadiya Haruna ta bayyana cewa ta dauki shawarar da wasu daga cikin jaruman masana’antar Kannywood suka bata, kan ta daina magana bisa dambarwar da ta kaure tsakaninta da jarumi Isa A. Isa.

Yayin da wasu ke ganin cewar kamar an fara sulhu a tsakanin su da jarumi Isa A. Isa.

Ashe abun ba haka yake ba ganin yadda jarumin Isa A. Isa ya dage kan cewar sai kotu ta kwato masa hakinsa na bata masa suna da ‘yar soshiyal midiyan ta yi wato Sadiya Haruna.

RUBUTU ALAKA:

An fara sulhu tsakanin jaruman da suka yi auren mutu’a

Yadda akayi auren mutu’a a Kannywood

Kun san abinda ya hana jaruma Maryam Yahya aure?

A yau ne dai Kotun majistret mai lamba 15 karkashin mai shari’a Muntari Garba Dandago ta aike da wata mata mai suna sadiya Haruna gidan gyaran hali.

Tun da farko ‘yansanda ne suka gurfanar da ita bisa zargin bata suna laifin da ya saba da sashi na 391 na kundin hukunta masu laifin Penal code.

Kunshin tuhumar ya bayyana cewar wani mashiryin shirin Hausa mai suna Isa A Isa shine yayi korafin akan cewar sadiyar ta bata masa suna.

Yayin da aka karanta kunshin tuhumar a gareta sadiyar ta musanta zargin da ake mata.

Lauyan wacce a ake kara Y A Sharif ya roki a sanya ta a hannun beli, inda ya buga misali da sashi na 35 da na 36 na kundin tsarin mulki wanda aka yiwa gyaran fuska a shekarar 2011.

Sai dai mai gabatar da kara Jacob ya yi suka inda ya bayyanawa kotun cewar da zarar an bayar da belin wadda ake zargin za ta iya kawo tarnaki a binciken da ‘yansanda sukeyi ko kuma ta tserewa shari’a.

Mai sharia Muntari Dandago ya sanya ranar juma’a dan yin kwarya-kwaryar hukunci akan rokon beli ya kuma yi umarnin a tsare ta zuwa waccan rana.

Wakilin mu Yusuf Nadabo Isma’il ya zanta da mai kara Isa A Isa Wanda yayi Karin haske kan zargin da Sadiya tayi masa.

Duk wani yunkuri da wakilin namu yayi dan jin ta bakin sadiyar abin ya faskara sai dai a cikin kotun ta bayyanawa alkalin cewar wannan zargi bashi da tushe, balantana makama.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!