Labaran Kano
An cafke direban da ake zargin yayi sanadin mutuwar jami’in KAROTA
Jami’an da ke aiki a sashin Operation Puff-Adder ne dai suka samu nasarar kame mutumin, wanda a kwanakin baya ya take wani jami’in hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA mai suna Tijjanai Adamu mai shekaru 27, inda kuma ya tsere bayan da ya bi ta kansa da mota.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa direban ya yi sanadiyyar mutuwar jami’in na KAROTA Tijjani Adamu, a mahadar El-Dorado dake Airport Road yayin da jami’in ke kokarin kwance lambar Motar a ranar 29 ga watan Oktoban da ya gabata.
Da yake gabatar da tambayoyi da aka nada ga direban a jiya Juma’a, kakakin rundunar ‘yan sands ta jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana cewa wanda ake zargin mai suna Alkasim Hussain, dan shekara 27 wanda mazaunin yankin Unguwa Uku ne, an kama shi a maboyarsa dake unguwar Farm Centre a Kano.
Haka kuma ya kara da cewa jami’an na Operation Puff-Adder karkashin jagorancin shugaban ofishin ‘yan sanda na Bompai, SP Daniel Itse Amah, sun kuma gano motar da ya kade marigayin da ita kirar Peugeot 307 dauke da daya lambar a jikinta mai harufa HZ 998 EKY.
Da yake bada amsa ga rundunar ‘yan sandan, wanda ake zargin ya amsa cewa shi ne ya take shi da motar amma ba da saninsa ya yi hakan ba.
Haka kuma ya kara da cewa motar ba tasa ba ce shi bakanike ne mai ita ne ya bashi gyaranta, kuma bai sanar da shi cewa ya aikata laifin ba.