Jigawa
An cafke wasu ‘yan damfara na banki a Jigawa
Rundunar ‘Yan sandan ta Jihar Jigawa ta samu nasarar damke wasu ‘yan damfara a Banki, wadanda su ke damfarar mutanen da basu iya amfani da kati nan cirar kudin ba da sunan temako.
Wani direban motar haya ne ya kai rahoton cewa ya aika yaron sa da ATM na bankin UBA a Dutse don ya ciro masa 25,000 sai yaron ya dawo yace masa katin ya makale.
Koda ya garzaya Bankin don sanar dasu katin sa ya makale, sai aka samu wani ya yi awon gaba dashi, jim kadan sai yaga sakon an cire masa dubu arba’in daga asusun ajiyar sa, ta hanyar yin amfani da katin cirar kudi na Banki access.
Bayan da rundunar Yan sandan ta fara bincike a kai ta samu nasarar kamo wasu matasa biyu da take zargin suna da hanu wajen yin wannan damfara.
Matasan da rundunar ta kama sun hada Isaac Izan mai shekaru 27 da kuma Emmanuel Ijeku mai shekaru 22, wadanda dukkan su yan unguwar Wunti ne ta jihar Bauchi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa SP Abdu Jinjiri yace tini suka fara bincike, kuma harma sun samu kudin da kuma katin cirar kudin a gurin yan damfarar, wanda direban yakai rahoto kuma nan bada jimawa ba za su dauki mataki na gaba.
You must be logged in to post a comment Login