Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An ci gaba da sauraron shari’ar faifan bidiyon Dala

Published

on

Babbar kotun jiha da ke Miller Road ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Sulaiman Baba Na Malam ta ci gaba da sauraron shari’ar faifan bidiyon Dala.

A yayin zaman na yau Litinin lauyan Ja’afar Ja’afar da na jaridar Penlight sun kawo suka kan yadda ɓangaren Ganduje ya shigo da sabbin lauyoyi waɗanda ba dasu aka fara shari’ar ba.

Sai dai mai shari’ar ya yi watsi da sukar ta su, tare da sanya ranar 20 ga watan Afrilu mai zuwa domin ci gaba da sauraron shari’ar.

Bayan kammala wakilin mu Bashir Muhammad Inuwa ya zanta da lauyan Dr. Abdullahi Umar Ganduje Barista Nassarawa wanda ya ce, su ba sababbin lauyoyi suka kawo ba, a’a ƙari ne suka yi cikin lauyoyin da ke kare su.

A nasa ɓangaren lauyan Ja’afar Ja’afar U.U Ete ya ce, daman sun kawo sukar ne ganin yadda aka zo baƙin fuska maimakon Barista Nura Ado Ayagi da aka faro shari’ar da shi ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!