Labaran Wasanni
An dage gasar Madrid Open ta gasar Tennis
Mahukuntan shirya gasar Tennis ta Madrid Open , sun sanar da soke gudanar da gasar a bana , sakamakon cutar Corona.
Mahukuntan sunce basu da tabbaci na bada cikakkiyar kariya ga masu halartar gasar , don haka suka soke gudanar da ita.
Gasar wacce da aka shirya gudanar da ita daga ranar 12 zuwa 20 ga watan September , ta sake samun tasgaro bayan tun da fari an shirya a gudanar da ita a watan Mayu daga 1 zuwa 10 ga shi.
Labarai masu Alaka.
An dakatar da wasan Tennis saboda barazanar cutar codiv 19.
Za’a dawo gasar wasan Tennis ta US Open a bana ba tare da ƴan kallo ba
Rahotanni sun tabbar da cewar, mahukuntan gasar sun samu umarni daga ma’aikatar Lafiya ta kasa cewar kar a gudanar da gasar sakamakon cutar na kara yaduwa.
Mahukuntan sun tabbatar da dakatar da gasar wacce za ayi da a Caja Magica, na Madrid kana shekarar badi za a gudanar da ga 30 ga Afrilu zuwa 09 ga watan Mayu.
A cewar shugaban gudanar da gasar Feliciano Lopez , “Munyi iya bakin kokarin mu don gasar ta tabbata , sai dai rashin tabbasa ya sa dole mu hakura, muna baiwa kowa da kowa hakuri da fatan zamu hadu a shekara ta gaba “.
Soke gasar ,ya sa a bana ba za a gudanar da babbar gasa ta WTA ba , bayan soke gasar Indian Wells da Miami Open sai China Open.
You must be logged in to post a comment Login