Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Fulham ta dawo gasar Firimiyar Ingila daga rukuni na daya

Published

on

 

Kungiyar kwallon kafa ta Fulham , ta samu tikitin dawowa gasar Firimiyar Ingila ta kakar badi da za a fafata 2020/21.

Hakan ya biyo bayan nasarar data samu yanzu a wasan neman cancanta daya gudana tsakanin ta da takwarar ta , ta Brentford bayan ta doke ta da ci 2 da 1.

Tun da fari dan wasa Joe Brayn ne ya samu damar zura kwallo a minti na 105 na Karin lokaci , kafin daga bisani ya kara ta biyu a minti na 117 , sai dan wasan Brentford Henrik Dalsgaard da ya ramawa tawagar sa kwallo a minti na 120 ana dab da a tashi.

Nasarar ta Fulham, a filin wasa na Wembley na zuwa ne shekara daya bayan da Fulham ta fada zuwa rukuni na daya wato Nationwide a gasar kakar 2018/2019.

Inda a bangare daya kungiyar Brentford zata cigaba da kokarin hawa gasar rukunin Firimiya da ya gagareta tun tsawon shekaru 73.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!