Labarai
An dage sauya shekar Gwamna Abba zuwa 12 ga Janairu

Rahotannin da ke cewa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, zai fice daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar APC an dage shi, kamar yadda jaridar PlatinumPost ta rawaito.
A cewa wasu majiyoyi masu tushe na kusa da gwamnan sun bayyana cewa ranar da aka fara tsara wa domin sauyin sheƙar a hukumance, wato Litinin, 5 ga Janairu, 2026, yanzu an sauya ta zuwa Litinin, 12 ga Janairu, 2026.
A baya, jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa Gwamna Yusuf zai sauya sheƙa zuwa APC a ranar 5 ga Janairu.
Sai dai wata majiya mai tushe, wadda ta nemi a sakaya sunanta kuma ta halarci wani taro tsakanin Gwamna Yusuf da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, a Abuja ranar Juma’a, ta bayyana cewa gwamnan ya nemi ƙarin lokaci.
A cewar majiyar, Yusuf na son ci gaba da tuntubar wasu ‘yan majalisar dokokin jihar da sauran manyan masu ruwa da tsaki da har yanzu ba su bayyana cikakken goyon bayansu ga wannan yunƙurin siyasa ba.
You must be logged in to post a comment Login