Siyasa
An dage taron majalisar zartaswa sakamakon yakin neman zabe
Rahotanni sun bayyana cewa ba’a gudanar da taron majalisar zartaswa ba, wanda aka saba gudanarwa a duk ranar Laraba Sakamakon kamfen da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya je jihar Ebonyi da Cross River.
Wannan dai shi ne karo na biyu da ake kin gudanar da zaman duk saboda rashin samun sukunin zuwan na shugaban kasa Muhammadu Buhari biyo bayan yawon kamfen da shugaban kasa da mataimakin sa suke yi a yanzu zuwa jihohi.
Bisa al’ada dai idan shugaban kasa Muhammadu Buhari bai samu sukunin zuwa taron ba mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo ne ke jagorantar zaman.
A makon da ya gabata ma dai ba’a gudanar da zaman ba, sakamakon cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari yana jihar Sokoto a wani bangaren na yakin neman zabe yayin da mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo ke gudanar da yakin neman zabe na gida-gida da ake kira da House to House Campaign.
Sai dai da ya ke jawabi mataimakin shugaban kasa kan harkokin yada Labarai Femi Adesina ya ce babu wata doka da ta ce dole ne a gudanar da taron majalisar zartsawa a kowanne mako, inda ya buga misali da zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar-Adua da ake gudanar da taron duk bayan mako biyu.