Connect with us

Kaduna

An dakatar da ƴan majalisa uku a Kaduna

Published

on

Majalisar dokokin jihar Kaduna, ta dakatar da tsohon mataimakin shugaban majalisar Muktar Isa Hazo da wasu ƴan majalisa biyu har tsawon wata tara.

Dakatarwar ta biyo bayan karɓar rahoton kwamitin ɗa’a na majalisar a Talatar nan.

Kwamitin ya zargi ɗan majalisa mai wakiltar Kagarko Nuhu Goro da Yusuf Liman dake wakiltar Maƙera da kuma Muktar Isa Hazo dake wakiltar Basawa da yunƙurin juyin mulki a majalisar.

Haka kuma kwamitin ya buƙaci wasu ƴan majalisar biyar da a baya aka zarga da shiga cikin wannan juyin mulki da su rubuta takardar baiwa majalisar hakuri a shafukan manyan jaridun kasar a bisa laifin da suka aikata na kawo yamutsi a majalisar.

Ƴan majalisun da aka umarta da su bada hakurin, sun haɗa da tsohon shugaban majalisar Aminu Abdullahi Shagali da  Salisu Isa da kuma Nasiru Usman.

Sai kuma Yusuf Salihu Kawo da kuma Abdulwahab Idris Ikra

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!