Labaran Wasanni
An dakatar da gasar Firimiyar kasar Ingila sabo da-Corona
Hukumar shirya gasar premier ta kasar Ingila ta sanar da dakatar da gudanar da gasar firimiya ta kasar sakamakon barazanar yaduwar cutar Coronavirus.
Hukumar ta sanar da cewar za’a dawo gudanar da gasar ne ranar 04 ga watan Afrilu bana.
Ana dai zargin ‘yan wasan kwallon kafa da dama a kasar ta Engila na dauke da kwayar cutar mai lakabin Covid 19.
Sanarwar, dakatarwar ta shafi dukkanin wasannin da ake bugawa a gasar da karamar gasar sai ta mata da gasar FA.
Dakatar da gasar ya biyo bayan shawarwari da hukumar shirya gasar tayi da likitoci wanda suka ce cigaba da gudanar da gasar ka iya haifara da hatsarin kamuwa da cutar.
Zuwa yanzu dai kasashe da dama a nahiyar turai sun dakatar da gudanar da wasannin kwallon kafa da suka hadar da gasar Serie A ta kasar Italiya da Laliga ta kasar Spaniya sai Bundesliga ta kasar Jamus da ligue 1 ta kasar Fransa.
Haka kuma masana kiwan lafiya a kasar sun baiwa kungiyoyi na wasanni a kasar shawarar kauracewa duk wani taron jama’a ko kuma taro tsakanin ‘yan wasa da ‘yan kallo da kuma ziyarar baki zuwa filayen wasanni.
You must be logged in to post a comment Login