Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An dakatar da sufurin jirgen sama na gida a Najeriya.

Published

on

Ƙungiyar masu jiragen sama ta Najeriya (AON) ta sanar da dakatar da ayyukanta, daga ranar Litinin 9 ga watan Mayun 2022.

Shugaban ƙungiyar Alhaji Abdulmunaf Yunusa Sarina ne ya bayyana hakan a wani sakon murya da aikewa Freedom Radio, inda yace hakan ya biyo bayan tashin farashin man jirgin daga Naira 190 zuwa 700 a kowacce lita.

Ya kuma ce tashin dala na daga cikin dakatarwar matuƙar gwamnati bata duba su ba, “Man da muke siya a Naira 90 yanzu ya koma 700, dalada muke siya 300, 320 ta koma 600 ba ma samunta da farashin gwamnati, ita kuma harka ta jirgin sama kashi 90 da dala ake tafiyar da ita, kuma maganar man jirgin nan mun yi kuka, mum yi kuka, mun zauna da shugabanni kala-kala a gwamnatance amma har yanzu babu abin da ya wakana, abubuwan sun mana zafi matuƙa, shi ne yasa muka ce, to bari mu saurara ko gwamnati zata yiwa masu man jirgin magana, mu riƙa samun mai sauƙi”.

Tuni dai ƙungiyar ta aikewa ministan sufurin jiragen sama Hadi Surika wannan koken, a wata takarda mai ɗauke da saka hannun shugaban ƙungiyar Alhaji Abdulmunaf Yunusa Sarina.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!