Labaran Wasanni
An dakatar da ‘yar wasan Najeriya Blessing Okagbare shekaru 10
An dakatar da ‘Yar wasan Najeriyar da ta samu lambar azurfa a shekarar 2008, Blessing Okagbare a ranar Juma’a 18 ga Fabrairu 2022 hukuncin shekaru 10.
Wannan dai na zuwa ne bayan da aka kore ta daga gasar wasannin motsa jiki ta Olympics da aka gudanar a birnin Tokyo a shekarar da ta gabata saboda kamata da laifin shan kwayoyi kara kuzari.
Hukumar kula da da’ar hukunta ‘yan wasa ta gasar Olympics (AIU) ce dai ta sanar da hakan a ranar Juma’a, bayan gudanar da binciki akan ‘yar wasan.
Hukuncin dai ya nuna cewa an dakatar da ita shekaru biyar na gaza halartar gasar, sai kuma laifin amfani da wasu haramtattun abubuwa saboda kin ba da hadin kai da binciken na AIU kan lamarin zargin da ake mata, wanda shima aka dakatar da ita shekaru biyar wato jumulla shekaru 10 kenan.
You must be logged in to post a comment Login