Labarai
An dawo da harkokin sadarwa a jihar Katsina
Gwamnatin jihar Katsina ta dawo da layukan sadarwa a ƙananan hukumomin da aka katse a kwanakin baya.
Mai bai wa gwamnan jihar shawara ta musamman kan harkokin tsaro Ibrahim Ahmad Katsina ya sanar da hakan ga manema labarai.
Ya ce, gwamnati ta yanke shawarar dawo da harkokin sadarwar ne biyo bayan samun sauƙin ayyukan ta’addanci a yankunan da aka katse.
Sama da watanni 3 da gwamnatin jihar ta sanar da katse layukan sadarwa a ƙananan hukumomi 17 na jihar da suke fuskantar matsalolin tsaro.
Gwamnatin ta ce ta dauki matakin ne domin daƙile ayyukan ta’addanci da masu bai wa yan ta’addar bayanan sirri.
Ko a ranar Larabar makon nan, rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta hannun mai magana da yawun ta SP Gambo Isah ta ce gwamnatin jihar ta ba da umurnin a ci gaba da kasuwancin kananan dabbobi irinsu tumaki da awaki a kasuwannin da aka haramta kasuwancin dabbobi a jihar.
You must be logged in to post a comment Login