Labaran Kano
An fara aikin matatan tace dagwalon masana’antu a Kano
A jiya ne ma’aikatar muhalli da tawagar ma’aikatar Muhalli ta kasa da kamfanin da zai gudanar da aiki matatar dagwalon masana’antu da kamfanonin fata na rukunin Sharada da Challawa da Bompai su ka zo unguwar sabuwar gandu domin duba inda za’a dasha matatan.
Tuni dai wannan kamfani mai suna Messrs ya fara wannan aiki inda aka fara daga unguwar Sharada Phase 3 zai kuma kare a unguwar Sabuwar Gandu, ma’aikatan dai sun zo dubawa tare da shaidawa ‘yan unguwar aikin da zasu gudanar.
Wannan matata wato Secondary treatment plant zai taimaka ne wajen dauke matsanacin wari na dagwalon masana’antun da ke fitowa daga kamfanonin da ke wannan aiki, inda za’a samar da hanya daya da ruwan kamfanonin zai dinga bi, don kauracewa gurbatar muhalli.
Mataimakin Darakta na gurbatar ma’aikatar Muhalli ta jihar Kano Muhammad Baba Ahmad – ya ce wannan aiki kimanin shekaru goma da suka wuce ake ta fafatukar ganin aikin ya tabbata sai gashi a halin da ake ciki tuni aka fara shimfada bututu tun daga Challawa zuwa unguwar rukunnin masana’antu ta Sharada phase 3, har ya dangana zuwa nan bayan Unique dake daura da gidan Freedom radio.
Shin ina makomar matsalar gurbatar muhalli a Jihar Kano
Ya ce a asusun ayyukan da suka shafe muhalli wato ‘Ecological fund’ ne aka ware wannan aiki inda aka baiwa wani kamfani mai suna Messrs wanda aka zo da wakilai daga Abuja domin ganin yadda ake yake gudana.
Tun watan Maris din wannan shekara ne ake zaton an fara wannan aiki, a don haka ne aka zo da ma’aikata domin duba inda wadannan bututu zai bi.
Akwai dai batu na cewar wasu kamfanonin ba’a sanya su cikin wannan tsari domin fitar da wadannan bututu na tace dagwalon masana’antu kafi ya kai ga fita , sai y ace an hada wadannan ayyuka kuma za’a juna su sannan duk kamfanin da aka kama ya saba da kaidojin da aka gindaye musu za’a hukunta su.
Ya kara da cewa ba zasu yarda wadannan kamfanoni su gurbata muhalli ba tare da su fuskanaci fushi hukuma ba.
Abdulshakur Dabo shugaban kungiyar Sabuwar Gandu bangaren tsaro ya ce an ce an fara wannan aiki na samar da matatar dagwalon masana’antu amma aikin bai kai ga ganin idanunsu ba.
Domin kafin wannan lokaci sun shiga matsanacin hali, al,ummar yankin sun shiga cikan halin kakani-kayi inda da damda suka samu rashin lafiyar da suka dangana da asibiti.