Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

KannyWood

An fara sulhu tsakanin jaruman da suka yi auren mutu’a

Published

on

Fitacciya a kafar sadarwa ta Instagram Sadiya Haruna ta bayyana cewa ta dauki shawarar da wasu daga cikin jaruman masana’antar Kannywood suka bata, kan ta daina magana bisa dambarwar da ta kaure tsakaninta da jarumi Isa A. Isa.

Sadiya Haruna ta bayyana hakan ne a shafinta na Instagram, inda ta gode wa jaruma Hadiza Gabon tana mai cewa “Aunty Hadiza Gabon a koda yaushe ina alfahari da ke wallahi tallahi kalmominda kika gaya mun sun fi million 100 a gurina”.
Sai ka shiga matsala ne zaka gane mai sonka.
Kuma insha Allah ba zan sake cewa komai ba akan wannan batun nagode sosai ‘yar uwa”.

A jiya Lahadi ne jami’an ‘yan sanda a jihar Kano suka bada belin Sadiyar bayan da suka kamata bisa korafin da jarumi Isa A. Isa ya shigar kan zargin ta ci zarafinsa.

Rubutu masu alaka:

Kun san abinda ya biyo bayan komawar Aisha Buhari Villa?

Kun san abinda ya hana jaruma Maryam Yahya aure?

Yadda akayi auren mutu’a a Kannywood

A zantawar Freedom Radio da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da bada belin nata yana mai cewa, rundunar za ta cigaba da bincike kan lamarin.

Sai dai a wani sautin muryar waya dake yawo a kafafen sada zumunta ya bayyana muryar Isa A. Isa din inda yake cewa kotu ce kawai zata raba su da Sadiyar bisa kazafin da tayi masa.

Haka ma dai wani bidiyon kira (video call) dake yawo a shafukan na sada zumunta sun nuna Sadiyar tana tattaunawa da wani, inda take musanta cewa ‘yansanda sun kama ta.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!