Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

An fidda alkaluman gasar firimiya ta kasa zuwa wasannin mako na ashirin da biyu

Published

on

 

Hukumar shirya gasar lig  ta kasa  LMC, ta fitar da alkaluman yawan wasan da akayi da kuma yawan kwallaye da aka zura kawo yanzu haka.

Daga fara gasar zuwa mako na ashirin da biyu, anyi wasa Dari biyu da sha shi da, tare da zura kwallaye Dari hudu da talatin da biyu.

Kungiyoyin da suka yi wasa a gida sun zura kwallaye dari uku da daya, sai wanda suke baki da suka zura Dari da talatin da daya, akalla ana zura adadin Kwallo biyu a duk wasa daya.

An kuma samu katin gargadi na ruwan dorawa wato Yellow card , guda dari bakwai da sha biyar, sai katin kora wato Jan kati Red card, ashirin da biyar.

Labarai masu kamanceceniya

SWAN ta kafa kwamitin sulhu a Kano

Kano Pillars ta samu nasara karon farko a kakar wasanni ta bana

 

An samu nasara a gida guda dari da hamsin da tara, a waje kuma ashirin da bakwai, tare da samun canjaras hamsin da bakwai, sai Kwallo da aka ci gida da kai ,wato own goal guda hudu.

Hukumar ta LMC, tace an  samu zura kwallaye biyu da mutum daya ya ci, ‘brace ‘sai kwallaye uku wato hattrick, guda biyu ,bugun daga kai sai mai tsaron raga wato Penalty, arba’in da tara , inda aka zura guda arba’in tare da zubar da guda tara.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!