Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

An sayi dan wasan Dambe naira dubu hudu a Kano

Published

on

Ba sabon abu bane wasan damben gargajiya dan wasa ya canja sheka daga wani yanki zuwa wani yanki bisa radin kanshi bata reda cinikayya kudade ba.

Sai dai a karon farko anfara gabatarda cinikin dan wasan damben gargajiya na yankin Arewa Dan Inyamurin shagon shagon bahagon Balangada , zuwa yankin Kudu, iyalan dan China kan zunzurutun kudi naira dubu hudu.

Sakataren kuungiyar magoya bayan ‘yan wasan Damben kudawa na jihar kano Ibrahim Doctor shine ya jagoranci wannan ciniki.

Bayan gama cinikin ne dan wasan da aka siya, ya canza sunan sa daga Shagon Shagon Bahagon Balangada zuwa Shagon Shagon Jafaru.

A baya bayan nan bangaren Kudu sun ta ba kokarin zawarcin dan wasan damben Gurumada Bahagon Maitakwasara, amma hakan su bai cimma Ruwa ba.

A nasu bangaren , suma ‘yan Arewa suna zawarcin dan wasan bangaren yankin Kudu, Gurumada Shagon Bahagon mai Bulala.

A dai wasan damben dake gudana a filin wasa na Ado Bayero Square ,dake unguwar Sabongari , ranar Lahadi mai zuwa ne za,a fafata wasan karshe na gasar Damben Motar Kwamishinan Matasa da wasanni na jihar Kano Kabiru Ado Lakwaya, tsakanin Autan dan Bunza da Dan Alin bata Isarka.

Karin labarai:

‘Yan damben Arewa da kudu sun dambata a Kano

DAMBE: Bahagon Wada ya lashe kyautar mashin

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!