Labaran Kano
SWAN ta kafa kwamitin sulhu a Kano
Kungiyar marubuta labaran wasanni ta kasa reshen jihar Kano ta kafa wani kwamiti na mutane uku da zai jagoranci sulhu a tsakanin mambobin kungiyar da aka samu sabani.
A ranar 8 ga watan Octoban da ya gabata ne kungiyar ta gabatar da zaben shuwagabannin kungiyar na shiyyoyin kasar nan a garin Fatakwal, inda aka zabi Lirwanu Idris Malikawa Garu a matsayin mataimakin shugaban kungiyar na kasa shiyyar Arewa maso yamma.
Sai dai wani rikici da ake zargin ya faro tun kafin lokacin zaben tsakanin tsohon mataimakin shugaban kungiyar shiyyar Arewa maso yamma Ado Salisu da kuma sabon mai mukamin na yanzu wato Lirwanu Idris Malikawa Garu.
A makon da ya gabata ne dai kungiyar ta SWAN reshen jihar Kano ta dakatar da Ado Salisun na dan wani lokaci, inda a jiya kuma ta kafa kwamitin sulhu na mutane uku wadanda suka hada da Tukur Arab, Salma Yusuf da kuma Aminu Abba Kwaru.
Karkashin wannan kwamiti dai ana sa ran zai jagoranci yin sulhu tsakanin tsoho da kuma sabon mataimakin shugaban shiyyar Arewa maso yamma.
RUBUTU MASU ALAKA:
‘Yan wasan Nigeria na ci gaba da taka rawar gani a gasar cin kofin Zakarun Nahiyar Turai
Yadda ma’aikata za su bibiyi hakkin su-hukumar kyautatuwar ma’aikata