Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

An fitar da sunan ‘yan wasan kungiyar  Super Eagles da zasu fafata da kasar Sierra Leone

Published

on

 

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles , Gernot Rohr, ya fitar da sunayen ‘yan wasa ashirin da hudu, da ya kira don tunkarar wasan da kasar nan zata fafata da kasar Sierra Leone ,a wasan share fagen shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za’ayi na shekarar 2021 a kasar Kamaru.

Wasan dai  za’a fafata a ranakun ashirin da bakwai da talatin da daya  na watan Maris , a filin wasa na Stephen Keshi dake birnin Asaba, da birnin Freetown na kasar ta Saliyo .

A wata sanarwa  da hukumar kwallon kafa ta Kasa, NFF, ta fitar ta bayyana sunan ‘yan wasan ashirin da hudu data ce Gernot Rohr ya gayyata don fafatawa a wasan.

Yan wasan sun hada da, masu tsaron gida , Daniel Akpeyi daga kungiyar Kaizer Chiefs ta kasar Afirka ta Kudu (South Africa) sai Ikechukwu Ezenwa daga Heartland , da Maduka Okoye daga kungiyar Fortuna Dusseldorf daga kasar Jamus (Germany ).

Ya yin da ‘yan wasan baya ,suka kasance da Kenneth Omeruo,daga CD Lagenes ta kasar Andalus wato Spain, Leon Balogun daga Wigan din kasar Ingila, Chidozie Awaziem daga CD Leganes, William Ekong daga kungiyar Udinese dake Italiya, Olaluwa Aina a  Torino dake Italiya, Jamiu Collins daga Paderborn ta kasar Jamus, Oluwasemilogo Ajayi daga kungiyar West Bromwich Albion , daga kasar Ingila, sai Kingsley Ehizibue, daga Fc Koln dake Jamus.

Labarai masu alaka

Dalilan dakatar da wasanni a birnin Tokyo

Tsohon dan wasan kungiyar super eagles ya bukaci mai horas da kungiyar lalubo hanyar atisaye na musssaman

Sai ‘yan wasan tsakiya da suke da Shehu Abdullahi daga Bursaspor ta kasar Turkiyya, Oghenekaro Etebo na  Getafe ta kasar Andalus, sai Wilfred Ndidi daga Leicester City dake Ingila, Joseph Ayodele Aribo, na Rangers din kasar Scotland, tare da Ramon Azeez dake  kungiyar Granada  kasar Andalus.

Daga masu zura Kwallo a raga, wato ‘yan gaba, sun kunshi Ahmed Musa dake taka Leda a Al Nassr, ta kasar Saudi Arabia, Alexander Iwobi daga Everton ta Ingila, sai Victor Osimhen daga Lille ta kasar Faransa, tare Samuel Chukwueze, na kungiyar Villarreal a kasar Andalus, sai sabon dan wasa Cyril Dessers daga Heracles Almelo dake Kasar Netherlands, da Kelechi Eheanacho na kungiyar Leicester City ta kasar Ingila , sai Samuel Kalu na Girondins Bordeaux dake kasar Faransa.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!