Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

An cafke Ronaldinho a kasar Paraguay bisa zargin fasfon bogi

Published

on

Hukumomi a kasar Paraguay, sun kama tsohon gwarzon dan wasan duniya dan kasar Brazil, Ronaldinho bisa zargin sa da amfani da fason Bogi tare da shiga kasar ba bisa ka’ida.

Mai shekaru  39, Ronaldinho, wanda ya lashe kofin duniya da kasar sa a shekarar  2002, kasashen Japan da Korea,  an kama shi ne a wani gurin shakatawa na bakin Tafki,mai suna   Resort Yacht & Golf Club Paraguayo, tare da dan uwansa   Roberto, a daren jiya Laraba, kamar yadda sanarwar ma’aikatar harkokin cikin gida ta kasar Paraguay ta tabbatar.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, an samu fasfo din a dakin su na Otal, dashi da dan uwansa da sunayen su a jikin fasfo na kasar ta Paraguay.

Labarai masu alaka.

Yadda wasannin zakarun nahiyar Turai ke gudana

Shin kun san alkalin da zai busa wasan Nijeriya da Brazil?

 

Bayanai daga wajen ‘yan sandan kasar ta Paraguay, sun tabbatar da cewa Ronaldinho, da dan uwansa sun shigo kasar ne bisa gayyatar wani gidan rawa da shugaban sa  Nelson Belotti, ya,  yi musu don gabatar da tsohon dan wasan tare da ganawa da dumbin magoya baya,  da ‘yan jaridu da masu ruwa da tsaki a kwallon kafar kasar.

A baya hukumomi a kasar Brazil, sun zargi dan wasan da, dan uwan sa da yin gini ba bisa ka’ida ba a gefen kogi na Guaiba,a shekarar 2015,  wanda waje ne da a  ke kamun kifi , ba tare da samun lasisin yin haka ba, hakan ta sa a ka ci su tarar sama da fam miliyan shida, kimanin naira biliyan ashirin da takwas.

Hakan ta sa aka kwace fasfon shi na kasar Brazil a watan Nuwambar shekarar 2018,  tare da hana shi tafiye tafiye, sakamakon kin biyan tarar kamar yadda babbar kotun kasar Brazil ta nema.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!