Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Aruna Quadri ya tafi jinyar rauni na mako uku

Published

on

Dan wasan kasar nan na wasan kwallon Tennis, Aruna Quadri, ya tafi jinyar rauni na mako uku sakamakon rauni da ya samu a cinyar sa.

Aruna Quadri, wanda kwararren dan wasan Tennis ne, da ya wakilci kasar nan a gasa daban –daban ta kasashen duniya, ya samu raunin ne a wasannin samun cancantar shiga gasar wasannin Olympic,da ake gudanar wa a kasar Tunisia.

Labarai masu alaka.

Gwamnatin Kano za ta kashe sama da miliyan 98 a bangaren wasanni

Dalilan dakatar da wasanni a birnin Tokyo

Yanzu haka dai samun raunin nashi ya  sa dan wasan ya janye daga gasar Qatar Open, da ake fafatawa yanzu haka  can a  kasar ta Qatar.

Dan wasa Quadri, na fatan murmurewa akan lokaci don fuskatar wasannin gasar ta Olympic, in da yace zai yi duk mai yiwuwa wajen kula da lafiyar sa don komowa bakin daga akan lokaci.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!