Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

An gano karin mutane 389 dauke da Corona a Najeriya

Published

on

Hukumar dakile bazuwar cutuka ta kasa NCDC ta ce an samu karin mutane 389 dake dauke da cutar Covid-19 a sassa daban-daban na kasar nan.

NCDC ta bayyana hakan ne ta cikin kididdigar masu dauke da cutar Covid-19 da ta fitar a daren Larabar nan ta shafinta na Twitter.

Hukumar NCDC tace jihar Legas ce ke kan gaba inda aka samu karin masu dauke da cutar 256, sai jihar Katsina mai mutane 23, jihar Edo itama an samu karin mutane 22.

Jihar Rivers kuma an samu karin mutane 14, mutane 13 a Kano, sai jihar Adamawa da ta samu karin mutane 11, haka abin yake a jihar Akwa Ibom ma mutane 11.

An samu karin mutum 6 a jihar Kaduna, hakama abin yake a jihar Nassadawa inda nan ma aka samu karin mutum 6, mutum 2 a Gombe, mutum 2 Plateau, jihar Benue ita ma mutum 2 sai jihar Niger mutum 2, haka abin yake a jihar Kogi, ita kuwa yau ne rana ta farko da aka samu bullar cutar a jihar da mutum 2.

Jihar Oyo ma an samu mutum 2 sai Imo da aka samu karin mutum 1, jihar Borno ma mutum 1 sai jihohin Ogun da Anambra da kowacce ta samu karin mutum dai-dai.

Yazuwa yanzu jimillar wadanda suka kamu da cutar Covid-19 a Najeriya sun kai mutane 8,733.
2,501 daga ciki sun warke, sai mutane 254 da suka rasa ransu sanadiyyar cutar.

*BS*

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!