Labaran Kano
An gano yara 273 dake zaman kansu a Kano
Kungiyar tabbatar da tsaro da zaman lafiya da ake kira da Nigerian Peace Unity Progress reshen jihar Kano ta bayyana cewa ta samu nasarar ceto kananan yara guda 273 dake rayuwa a kasuwannin jihar Kano.
Babban kwamandan kungiyar ta jihar Kano Ibrahim Adam Isah ya bayyana hakan a yayin taron daga likkafar wasu jami’an rundunar da ya gudana yau lahadi a nan Kano.
Ibrahim Adam ya bayyana cewa bisa binciken da suka gudanar sun gano yadda yaran ke rayuwa ta zaman kansu a kasuwannin Kantin wari, Kasuwar Kofar Wambai da kuma Kasuwar Sabon Gari da kuma wasu sassa na jihar Kano, ba tare da sahalewar iyayen su ba.
Kazalika Ibrahim Adam ya kara da cewa yara 27 ne kacal daga cikin 273 ‘yan asalin jihar Kano, yayin da sauran kuma suka shigo Kano daga makwabtan jihohi, har ma da wasu kalilan daga kasashe makwabtan Najeriya.
Tuni dai kungiyar tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro suka mika kananan yaran ‘yan jihar Kano zuwa ga iyayensu, sa’annan kuma sauran yaran aka mika su zuwa ga gwamnatocin jihohinsu.
Har ila yau, taron na kungiyar ta Nigerian Peace Unity Progress dai ya samu halartar iyayen kungiyar da suka hadar da dagatai da kuma jami’an ‘yan sanda, da lauyoyi masana shari’a.
Labarai masu alaka:
Ilimin ‘ya’ya mata zai gyara rayuwar al’umma –Yariman Kano
Kano9: Ina rokon mahukunta su magance satar yara -Sheikh Kariballah Kabara