Labarai
An haifi yara sama da dubu tamanin ciki wata biyu a Kano
- Yawan haihuwar da aka samu a jihar Kano ya karu daga dubu sittin da tara zuwa dubu tamamin da uku daga karshen watan disamba zuwa Junairu.
- An kuma samu raguwar mace-macen mutane a Kano.
Gwamnatin jihar Kano ta ce, yawan haihuwar da aka samu a jihar ya karu daga dubu sittin da tara zuwa dubu tamamin da uku daga karshen watan Disambar bara zuwa farkon watan junairun shekarar 2023 da muke ciki.
Daraktan kula da likitoci a hukumar kula da asibitoci jihar Kano Dakta Sulaiman Mudi Hamza ne ya bayyana hakan yayin tattaunawarsa da wakiliyar Freedom Radio, Safara’u Tijjani Adam da yake rabon magani da hukumar ta saba yi ga asibitocin jihar Kano.
Ya ce ya zuwa yanzu an samu raguwar mace-macen mutane da kananan yara a Kano, wanda hakan ke da nasaba da samun wadatattun kayayyakin kula da lafiyar al’umma.
A nata bangaren shugabar sashin bada agajin gaggawa a asibitin kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano Hajiya Hasana Ibrahim ta ce, ‘kayayyakin na tallafawa al’umma musamman ma wadanda suka gamu da hadari’.
Hukumar kula da asibitoci ta jihar Kano ta ce, za su ci gaba da sanya idanu domin ganin kayyakin da suka bayarwa asibitocin don yin amfani da su ga al’umma.
RAHOTO:Safara’u Tijjani Adam
You must be logged in to post a comment Login