Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kashe direban Tirela: Direbobi sun hana sifuri a hanyar Kano zuwa Zaria

Published

on

  • Tawagar direbobin tirela sun rufe hanyar Kaduna zuwa Kano sakamakon zargin kashe musu dan uwansu da wani jami’in soja ya yi a wajan wani shinge.
  • Sai dai direbobin sun yi zaman dirshen a kan hanya, suna ikirarin cewa ba za su bar hanyar ba, har sai an biyasu diyyar dan uwansu.
  • Ya zuwa wannan lokacin an kai gawar mamacin mai suna Abdulhamid Habib wani asibiti a Kaduna domin bincike.

 

Da safiyar yau ne Alhamis direbobin tirelar suka rufe babbar hanyar zuwa Kaduna, dai-dai unguwar Wambai a karamar hukumar Ikara, sakamakon zargin da suke yiwa wani jami’in soji ya kashe ‘dan uwansu.

Da misalin karfe tara da rabi na safiyar Laraba ne wani jami’in soja da ke bada tsaro ga wasu aikin titin dogo na Kaduna zuwa Abuja ya tsayar da direbobin manyan motocin, daga bisani ne kuma yayi harbi, wanda ya samu daya daga cikinsu a kirji, inda ya rasa ransa nan take.

Wani ‘dan uwan mamacin Habibu Usman ya shaidawa Freedom Radio cewa, ‘sakaci ne yasa hakan ta faru ga ‘dan uwanmu, don haka bazamu bude hanya ba sai an bi mana hakkin mu.

‘Wasu daga cikin direbobin sun ce ko magana bata hada wanda aka kashe da jami’in sojan ba, yana tsayar da su, ya harbe shi’.

Har ya zuwa yanzu dai ba wani yunkuri da aka yi na sulhunta tsakanin wadanda abin ya faru.

RAHOTO:Halima Wada Sinkin

 

 

 

 

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!