Labarai
An kama jami’in hukumar kula da gidan gyaran hali da ke safarar kwayoyi ga daurarru a Kano.
Jami’an hukumar kula da gidan gyaran hali ta kasa (NCS) a Kano sun kama wani jami’in hukumar da ake zargin sa da safarar miyagun kwayoyi da nauyinsa ya kai kilo 4.8 da wayoyi kirar Android a gidan gyaran hali na Kurmawa da ke birnin Kano.
A ranar alhamis da ta gabata ne aka samu hatsaniya a gidan gyaran halin sakamakon kwace wasu nau’ikan kwayoyi da wayoyi da ake zargin wani jami’in hukumar kula da gidan gyaran halin ya yi safarar su ta barauniyar hanya ga daurarru da ke jiran hukuncin kisa.
Rahotanni sun ce kwace kayayyakin jami’an hukumar su ka yi a ranar ya janyo barkewar hayaniya, inda kuma hukumomi suka dau alwashin gudanar da bincike don zakulo wadanda ke da hannu cikin faruwar lamarin
Mai magana da yawun hukumar anan Kano Musbahu Lawal Kofar Nassarawa ya shaidawa freedom radio cewa, jami’in nasu da ake zargi yana hada baki ne da wasu manyan dilolin kwaya a gari don safarar miyagun kwayoyin zuwa cikin gidan gyaran halin na Kurmawa.
A cewar sa shekaru biyu da suka wuce ne a shekarar 2019 aka dauki jami’in aiki a hukumar ta kula da gidan gyaran hali.
You must be logged in to post a comment Login