Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An kama wasu da ake zargi da yunƙurin tayar da rikici a yayin zaɓen cike gurbi

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Kano haɗin gwiwa da sauran jami’an tsaro sun tabbatar da kama wasu da ake zargi zasu shiga yankin ƙananan hukumomin ƙunchi Tsanyawa domin tayar da hargitsi a yayin zaɓen cike gurbi da yake wakana.

Kwamishinan yansandan jihar kano CP Muhammad Ussaini Gumel ne ya bayyana hakan yayin da yake yiwa manema labarai karin haske a yayin zagayen tabbatar da an gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali.

Kwamishinan yace cikin wa’inda aka kama akwai Abdurrazak Muhammad da ake kira da Mai Salati mazaunin ƙaramar hukumar Birni ya tabbatarwa hukumar ƴan sandan cewa wani da yake takarar ɗan majalisar ne mai suna Gwarmai ne ya ɗauki nauyin su.

Haka kuma CP yace yanzu haka zasuje domin yin bincike ga wannan ɗan takarar domin tabbatar da lamarin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!