Labarai
An kama ‘yan fashi da makami a jihar Nasarawa
Jami’an rundunar ‘yan sanda dake aikin sintiri na jihar Nasarawa sun kama wasu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne da satar mutane su 27.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar ta Nasarawa Bola Longe ya sanar da hakan ga manema labarai cewa an kama ‘yan fashin ne a wurare daban-daban cikin makwanni biyu da suka wuce.
Yayin da yake holan ‘yan fashin a shalkwatar rundunar dake birnin Lafia a jihar Nasarawa, Bola Longe ya ce daga cikin wadanda aka kama akwai wadanda suka kashe shugabanni al’ummar Odu wato Amos Obere.
Kwamishinan ‘yan sandan ya yi bayanin cewar, an kama wadanda ake zargin a wata mashaya ya yin da suke tsaka da holewa.
You must be logged in to post a comment Login