Labarai
An kashe mutane 3 tare da jikkata wasu 2 a sabon harin Plateau

Akalla muatne uku aka kashe a wani sabon hari da aka kai wa wasu iyalai yayin da biyu suka samu raunika a kauyen Te’ebe da gundumar Miango a karamar hukumar Bassa da ke jihar Plateau.
Wannan dai na zuwa ne bayan da aka hallaka wasu matafiya a garin mangun a makon da ya gabata, loakcin da suke kan hanyarsu ta zuwa daurin aure daga garin Basawa.
Wadanda abin ya rutsa da su, sun kasance manoma yan gida daya, inda suka gamu da ajalin nasu loakcin da suke cire Tumatur din da suka noma a gona.
Tuni dai aka garzaya da mutum biyun da suka samu mummunan raunika zuwa asibitin birnin Jos domin yi musu magani.
You must be logged in to post a comment Login