Ƙetare
An kawo ƙarshen tattaunawar da aka yi tsakanin Rasha da Ukraine

An kawo ƙarshen tattaunawar da aka yi tsakanin Rasha da Ukraine
An kawo ƙarshen tattaunawar da aka yi a baya bayan nan tsakanin Rasha da Ukraine a Istanbul ba tare da an fitar da wata muhimminiyar sanarwa ba.
Rahotonni sun bayyana cewa, bangarorin biyu sun ce sun amince da yin aiki tare wajen sake yin musayar fursunoni na sojoji da na farar hula.
Masu shiga tsakani na Ukraine sun ce, babu wata yarjejeniya da aka cimma a tattaunawar tsakanin ƙasashen biyu amma Kyiv a shirye ta ke ta tsagaita wuta a yanzu.
Sai dai rahotonni sun bayyana cewa, fadar Kremlin ta sha yin watsi da fatan samun gagarumin ci gaba, tana mai cewa bambancin da ke tsakanin ɓangarorin biyu suna da yawa don haka zai yi wuya a iya cimma yarjejeniyar zaman lafiya.
You must be logged in to post a comment Login